Irin wadannan ‘yan mata – ko da ba su da niyyar lalacewa – halin da suka fada yana barazana ga rayuwarsu. Idan ba a kawo dauki ba, bata gari za su ci gaba da amfani da wannan dama wajen lalata su.
Wannan ba labari ne na nesa ba. Wadannan marayu ne mata, wadanda mahaifiyarsu ta yi bakin kokari wajen rainonsu tun suna yara, ta tsaya tsayin daka wajen tarbiyyarsu. Amma yanzu, rayuwa ta bijiro da kalubale – Allah ya jarabce ta da yanayin da ya gagari karfinta.
Yanzu haka, wadannan yara na kwana a wurin da ba ya dace da mutum balle yara mata. Wannan ya sa bata gari ke kokarin amfani da damar wajen ketare haddin su. Abin takaici, dakin da suke ciki ya rushe, yanzu suna kwana a cikin akurkin kaji.
Wallahi labarinsu cike yake da tashin hankali da tausayi.
Ga cikakken bidiyon da ke bayani:
Ko kuma ka tura taimako – ko da naira ɗaya ce – zuwa wannan asusun:
Maibiredi Charity Foundation
茶 Account Number: 2045281721
Bank: FIRST Bank
Domin karin bayani:
Kira ko WhatsApp: 08069807496. Allah ya saka da alheri. Mu taimaka musu – ko da da addu’a ce ko da kuma raba wannan sakon.
